Binciken manazartan kayan ci da sha wato Nutritionist ya tabbatar da cewa ta'ammali da tafarnuwa na da matukar amfani wajen inganta kiwon lafiyar dan Adam. Cikin alfanun cin tafarnuwa akwai kara karfin kuzari ga ma'aurata.
Akasari ana amfani da tafarnuwa ne wajen a matsayin kayan kamshi da kara dandanon abinci, sai dai bincike ya tabbatar da cewa ana amfani da ita wajen rigakafin cututtaka bila adadin.
Legit.ng ta kawo wasu daga cikin amfanin tafarnuwa kamar haka:
1. Cutar asma
Tafarnuwa na da tasiri wajen rigakafi da rage radadin cutar asma, inda ake bukatar mai cutar a duk dare kafin ya kwanta barci, ya dafa tafarnuwa ya sha da madara. Haka ma, wanda cutar ta taso masa, za'a iya bashi nikakkiyar tafarnuwa.
2. Tari da sanyi
Ana amfani da tafarnuwa wajen rigakafin sanyi da tari inda ake bukatar mai fama da tari, ya tauna tafarnuwa ko kuma ya hadiye ta kai tsaye ba tare da hada ta da komai ba.
3. Atini da gudawa
Tafarnuwa na kashe kwayoyin cuta da ke cikin ciki wadanda akasari su ke janyo atini da gudawa.
4. Matsalar ido
Tafarnuwa ta kunshi sunadarai irinsu, quercetin, selenium da vitamin C wadanda duk suna taimakawa wajen rigakafin cututtukan da suka jibinci idanu musamman kumburi ko kuma kaikayi.
5. Hawan jini
An ribatar tasirin tafarnuwa wajen rigakafin cutar hawan jini inda aka lakanci amfani da ita akai akai. Sakamakon wani bincike ya nuna cewa man da aka tatse daga tafarnuwa na taimakawa mai cutar hawan jini daga kamuwa daga cututtukan da hawan jinin kan haifar.
KARANTA KUMA: Lafiyar hanta da sirrika 8 na ganyen gwanda a jikin dan Adam
6. Rage kiba
Tafarnuwa ta kunshi sunadarin allicin wanda ke kona kitsen da ke haddasa illa a jiki.
7. Narkewar abinci
Yawan amfani da tafarnuwa cikin abinci yana taimaka wa wajen saurin narkewar abinci a cikin ciki ta yadda sunadaran gina jiki za su yadu cikin jini a kan lokaci.
8. Kara karfin mazakuta ga namiji
Sakamakon wani bincike ya nuna tafarnuwa ya kunshi sinadarin Aphrodite wanda ke taimakawa ma'aurata wajen kuzari yayin saduwa da iyali.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9kW9samhpYrmissiymKtlmZm8brDAZpimnpGjtq9505qdmqqeqsSieZZmnpplnJazqsXAq2SdmZ5irqWtzGefraWc